Isa ga babban shafi

Trump na zargin shugaba Biden da sharewa Taliban fagen samun nasara

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya ce wanda ya gaje shi wato Joe Biden ne ya share wa mayakan Taliban fagen samun nasarar kwace muhimman yankuna daga dakarun gwamnatin Afghanistan.

Yan Taliban sun kaffa tutar su  a arewacin Kunduz na kasar Afghanistan
Yan Taliban sun kaffa tutar su a arewacin Kunduz na kasar Afghanistan - AFP
Talla

Trump, ya ce salon da Biden ya yi amfani da shi wajen janye dakarun Amurka daga kasar a cikin gaggawa kuma ba tare da wani sharadi ba, shi ne dalilin bai wa Taliban nasara.

Yankunan da suka fada hannun mayakan Taliban a Afghanistan
Yankunan da suka fada hannun mayakan Taliban a Afghanistan - AFP

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump a zamanin sa ya sha alwashi ci gaba da yakar yan taliban duk da cewa wasu Amurkawa na sukar matakin na Amurka na ci gaba da kashe makkuden kudade a fagen daga da ba shi da alfanu ga kasar ga baki daya.

Mayakan Taliban na ci gaba da samun nasarori,inda rahotanni daga kasar ke nuni cewa sun kama ikon birane 13,yayinda jama'a ke ci gaba da tserewa daga yankunan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.