Taliban ta kwace babban birnin lardi na farko a Afganistan
Kungiyar Taliban ta kwace iko da babban birnin lardi na farko a Afghanistan, nasarar farko da ta samu tun bayan kaddamar da farmaki kan dakarun gwamnati, a daidai lokacin da sojojin kasashen waje karkashin jagorancin Amurka suka fara ficewa daga kasar.
Wallafawa ranar:
Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP, Roh Gul Khairzad, mataimakiyar gwamnan Nimroz ta tabbatar da kwace ikon da Taliban tayi da Zaranj, babban birnin lardin.
Mataimakiyar gwamnan ta ce mayakan na Taliban sun karbe iko da birnin na Zaranj da ke kusa da kan iyaka da Iran ne ba tare sun fafata da dakarun gwamnati ba.
Bayanai sun tabbatar da cewa mamayar da Taliban ta yiwa Zaranj babban birnin lardin Nimroz, ta zo ne a daidai lokacin da mayakan kungiyar suka harbe shugaban sashen watsa labarai na gwamnatin Afghanistan a Kabul.
Matakan dai sun sha alwashin ci gaba da kai hari kan manyan jami'an gwamnati domin ramuwar gayya kan hare –haren da sojojin Afghanistan da na Amurka suka kaddamar kansu ta sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu