Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Taliban tayi alkawarin ci gaba da kai hari kan jami’an gwamnatin Afghanistan

Kungiyar Taliban tayi alkawarin ci gaba da kai munanan hare hare akan jami’an gwamnatin Afghanistan, kwana guda bayan ministan tsaron kasar ya tasallake rijiya da baya lokacin da suka nemi hallaka shi.

Karin karfin Hare -haren Taliban ya bata damar kame manyan hanyoyin tsallaka kan iyaka, da gundumomi da dama tare da kewaye manyan larduna a Afghanistan.
Karin karfin Hare -haren Taliban ya bata damar kame manyan hanyoyin tsallaka kan iyaka, da gundumomi da dama tare da kewaye manyan larduna a Afghanistan. FARSHAD USYAN AFP
Talla

Harin da aka kaiwa ministan tsaro Bismillah Mohammadi daren talata shi ne na farko kan birnin Kabul cikin watanni.

Sai dai tun cikin watan Mayu ake fafatawa tsakanin mayakan kungiyar ta Taliban da dakarun gwamnati a yankunan karkara, lokacin da sojojin kasashen waje suka fara aiwatar da matakin karshe na janyewa daga Afghanistan.

A baya bayan nan sojojin Afghanistan da na Amurka suka zafafa kai hare-hare ta sama kan masu tayar da kayar bayan, sai dai kungiyar Taliban ta ce harin na Kabul da ta kai a ranar Laraba shi ne martaninta kan farmakin da ake kai mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.