Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Sojin Afghanistan sun kara azama a kokarin kwato yankunan kasar daga Taliban

Dakarun gwamnatin Afghanistan sun yi mummunar arangama da mayakan Taliban a karshen mako, a daidai lokacin da ‘yan tawayen suka mamaye birane da dama tare da kaddamar da jerin hare-hare a fadin kasar.

An Afghan soldier keeps guard outside the United Nations Assistance Mission in Afghanistan compound in Herat a day after the mission was attacked
An Afghan soldier keeps guard outside the United Nations Assistance Mission in Afghanistan compound in Herat a day after the mission was attacked HOSHANG HASHIMI AFP
Talla

Daruruwan dakaru na musamman ne aka girke a birnin Herat da ke yankin yammacin kasar, yayin da hukumomin birnin Lashkar Gah suka bukaci karin sojoji domin shawo kan hare-heren mayakan na Taliban.

Bayanai na cewa, sojojin Afghanistan sun yi luguden wuta tare da kashe  gomman ‘yan Taliban akan titunan kasar.

Tun a farkon watan Mayun da ya gabata, dauki-ba-dadi ya tsananta  a Afghanistan bayan da Amurka ta fara janye dakarunta a zango na karshe daga kasar.

Taliban dai ta kwace yankuna da dama ciki kuwa har da kan iyakokin kasar, yayin da kuma ta fara kaddamar da farmaki kan manyan biranen kasar.

Kungiyar ta yi ikirarin cilla wasu shu’uman makaman roka zuwa birnin Kandahar a karshen mako, lamarin da ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a yankin.

Kungiyar ta ce, ta kai harin ne a dalilin luguden wutar da sojojin kasar suka yi wa mayakanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.