An kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Kandahar dake Afghanistan
Mayakan taliban sun kai hari filin tashi da saukar jiragen saman na Kandahar dake kasar Afghanistan, tareda cilla rokoki guda uku da suka lallata hanyar saukar jirage dake wannan birni.
Wallafawa ranar:
Kandahar ,daya daga cikin manyan biranen kudanci Afghanistan na daga cikin wuraren da ake gwabza fada yanzu haka tsakanin mayakan Taliban da dakarun kasar ta Afghanistan.
Rahotanni yan lokuta da cilla wadanan rokoki na nuni cewa biyu daga cikin rokokin da aka harba sun lallata titin da jirgin sama ke sauka a kai.
Mayakan Taliban sun sha alwashin kwace yankunan da gwamnatin kasar ke iko a kai,matakin da suka dau tun bayan da Amurka ta sanar da janye dakarun ta daga wannan kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu