Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mayakan Taliban sun kwace iko da manyan birane 3 a rana guda

Mayakan kungiyar Taliban na ci gaba da mamaye karin yankuna a arewacin Afghanistan, inda a ranar Lahadi suka kame wasu manyan biranen larduna uku, makwanni kalilan bayan kaddamar da farmaki kan dakarun gwamnati da ke manyan garuruwa.

Dakarun Afghanistan yayin shirin fafatawa da matakan Taliban a birnin Kunduz, kwana guda bayan da suka kwace birnin lardi na 2.
Dakarun Afghanistan yayin shirin fafatawa da matakan Taliban a birnin Kunduz, kwana guda bayan da suka kwace birnin lardi na 2. STR AFP/File
Talla

Kawo yanzu manyan biranen larduna 5 mayakan Taliban suka kwace a Afghanistan daga ranar Juma’a zuwa Lahadi, alamar da ke nuna zai yi wuya dakarun gwamnatin kasar su iya murkushe su ba tare da tallafi ba.

Taloqan, Kunduz da Sar-e-Pul su ne manyan biranen lardunan da Taliban ta mamaye a ranar ta Lahadi, inda wasu majiyoyi suka ce sun samu nasarar ce ba tare da yin wani kwakkwaran gurmuzu da dakarun gwamnati ba.

Kame biranen Taloqan da Kunduz ce nasara mafi girma da Taliban ta samu kan gwamnatin Afghanistan a baya bayan nan, tun kaddamar da farmaki kan sojojin kasar a watan Mayu, a daidai lokacin da dakarun kasashen waje suka fara janyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.