Isa ga babban shafi
Amurka - Taliban

Amurka ta yi kira ga Taliban kan mutunta alkawuranta na kare hakkokin bil'adama

Amurka ta yi kira ga 'yan Taliban da su cika alkawuran da suka dauka na mutunta hakkokin ‘yan Afghanistan ciki har da mata, bayan karbe mulkin kasar da suka yi a wannan mako. Kiran na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da sauran kasashe da hukumomi ke nazarin makomar alakarsu da kungiyar ta Taliban.

Tawagar Taliban bisa jagrancin Mullah Abdul Ghani Baradar, da ta halarci zaman tattaunawar Moscow, na kasar Rasha don rattaba hanu kan yarjejeniyar zaman lafiya 18/03/21
Tawagar Taliban bisa jagrancin Mullah Abdul Ghani Baradar, da ta halarci zaman tattaunawar Moscow, na kasar Rasha don rattaba hanu kan yarjejeniyar zaman lafiya 18/03/21 AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a yau, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya bayyana fatan Taliban ta cika alkawarin da ta dauka, yayin taron manema labarai na farko da ta yi a jiya, inda ta ce za ta kare hakkin dan adam a bisa tsarin addinin Musulunci.

Yanzu haka dai hukumomin kasa da kasa na ci gaba da nazari kan yadda alakarsu za ta kasance da gwamnatin da kungiyar Taliban ke shirin kafawa, inda a ranar Juma’a ministocin kasashen da ke kungiyar tsaro ta NATO za su gana ta kafar bidiyon intanet kan halin da ake ciki a Afghanistan.

Shi kuwa babban babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Tura Josep Borell cewa yayi ya zama dole su tattauna da kungiyar Taliban da a yanzu ke rike da madafun ikon Afghanistan, la’akari da nasarar da suka samu, bayan rushewar gwamnatin da kasashen yamma ke marawa baya.

A wannan Laraba Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce tana karbar bakuncin tsohon shugaban Afghanistan Ashraf Ghani bisa dalilan jin kai, bayan da ya tsere daga kasarsa yayin da 'yan Taliban suka kwace iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.