Isa ga babban shafi
Taliban - Turai

Faransa da Birtaniya sun gargadi gwamnatoci kan gaggawar amincewa da Taliban

Birtaniya da Faransa sun gargadi kasashen duniya kan gaggawar amincewa da gwamnatin kungiyar Taliban mai iko da Afghanistan a yanzu, inda suka ce kamata ya yi a fara nazartar ayyukan da za ta gabatar, kafin fayyace makomar shirin kulla alaka da ita.

Kakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid, yayin taron manema labarai na farko tun bayan karbe iko da kasar Afghnaistan 17/08/21.
Kakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid, yayin taron manema labarai na farko tun bayan karbe iko da kasar Afghnaistan 17/08/21. AP - Rahmat Gul
Talla

Yayin jawabin da ya gabatar a wannan Talata, Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya ce za su yankewa sabuwar gwamnatin Taliban hukunci ne bisa la’akari da ayyukansu ba kalamai ba, a dangane da batutuwan da suka hada da ta’addanci, baiwa jami’an agaji damar shiga Afghanistan da kuma, mutunta hakkin mata wajen samun ilimi.

To shi ma dai yayin martani kan taron manema labaran da Taliban ta yi a jiya, ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya ce sun sa ido don ganin ko gwamnatin Taliban da ta mamaye Afganistan za ta kiyaye 'yancin da aka kafa a cikin kasar.

A wannan Talata ne dai kungiyar Taliban ta gudanar da taron manema labarai na farko tun bayan sake kwace iko da Afghanistan, shekaru 20 bayan korar ta da Amurka tayi.

Taliban din ta yi shelar kawo karshen yakin kasar, tare da sanar da yiwa dukkanin masu adawa da ita afuwa, zalika kakakin kungiyar Zabihulla Mujahid ya yi alkawarin baiwa mata damar gudanar da ayyuka bisa tsarin addinin Musulunci, sabanin suka yi yayin mulkinsu na baya fiye da shekaru 20 da suka gabata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.