Isa ga babban shafi
Taliban-Amurka

Biden ya kare matakin Amurka bayan nasarar Taliban a Afghanistan

Shugaba Joe Biden ya yi kakkausan suka ga tsohuwar gwamnatin shugaba Ashraf Ghani da ya fice daga Afghanistan, kan gaza yakar Taliban, abinda ya baiwa kungiyar damar sake kwace iko da daukacin kasar. Biden ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar a daren jiya kan halin da Afghanistan ke ciki.

Shugaban Amurka Joe Biden a jawabinsa bayan nasarar Taliban ta kwace iko da Afghanistan.
Shugaban Amurka Joe Biden a jawabinsa bayan nasarar Taliban ta kwace iko da Afghanistan. Brendan SMIALOWSKI AFP
Talla

Yayin jawabin da ya gabatar daga Fadar White House shugaban Amurkan ya ce yana nan daram kan matakin na janye dakarun kasarsa daga Afghanistan, domin kuwa bayan shekaru 20 suna gwabza yaki da kungiyar Taliban, ya tabbatar cewa babu lokacin da ya dace ya janye dakarun Amurka daga kasar kamar a wannan yanayi.

Biden ya ce babbar manufar da ya sa gaba ita ce kawo karshen yakin Afghanistan da ya zarce wa’adin da Amurka ta diba don ladabtar da Taliban saboda baiwa kungiyar Al-Qa’eda mafaka, bayan hare-haren ranar 11 ga watan Satumba da mayakan Al-Qa’edan suka kaiwa Amurkan.

Shugaban ya kara da cewar dama can dakarun Amurka basu shiga Afghanistan da nufin sake gina kasar ba, sai dai ya ce duk da janyewar da suka yi, za su cigaba da aikin kakkabe ‘yan ta’adda a kasar.

Biden ya kuma ce za a kwashe dubban Amurkawa da 'yan Afghanistan da suka yi aiki tare da sojojin Amurka a cikin kwanaki masu zuwa, tare da yin barazanar maida martanin soji idan mayakan Taliban suka kaddamar da farmaki a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.