Isa ga babban shafi
Taliban-Birtaniya

Gazawar Duniya ce ta sanya Taliban kwace Afghanistan- Birtaniya

Birtaniya ta bayyana kwace ikon da Taliban ta yi da Afganistan a matsayin gazawar kasashen duniya tare da zargin yammacin Turai da rashin hangen nesa a siyasance. Wannan na zuwa ne a yayin da sake fadawar Afghanistan hannun Taliban ya tilastawa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zama na musamman.

Dakarun Taliban a titunan birnin Kabul.
Dakarun Taliban a titunan birnin Kabul. Wakil Kohsar AFP
Talla

Yayin da ya ke tsokaci kan halin da Afghanistan ke ciki sakataren tsaron Birtaniya Ben Wallace ya ce yakin shekaru 20 da Amurka ta jagoranta a kasar ba asara ba ce.

A wannan Litinin ne dai kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya tattauna kan halin da kasar Afghanistan din ke ciki, musamman dangane da kare hakki dan adam ciki har da makomar ‘yancin mata da kuma dakile yunkurin ‘yan ta’adda na maida kasar cibiyarsu.

A gobe Talata kuma ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar Tarayyar Turai za su yi tattaunawar gaggawa ta bidiyo duk dai kan halin da ake ciki a Afghanistan, a yayin da kasashen Turan ke gaggawar kwashe ma’aikata daga kasar.

Ita kuwa China cewa ta yi a shirye take ta karfafa alakar hadin gwiwa da Afghanistan.

Kasar ta Sin da ta yi iyaka mai nisan kilomita 76 da Afghanistan, ta dade ta na fargabar makwabciyar ta ta na iya zama matattarar tsirarun 'yan kabilar Uyghur' Musulmi a yankin na kan iyaka da ke lardin Xinjiang.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.