Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Al'ummar Afghanistan na tururuwar fita daga Kabul saboda Taliban

Dubunnan al’ummar Afghanistan na ci gaba da tserewa daga birnin Kabul bayan da mayakan Taliban suka kwace iko da yankin dai dai lokacin da shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga kasar tun a yammacin jiya lahadi.

Wasu al'ummar Afghanistan da ke tururuwar ficewa daga Kabul babban birnin Kasar.
Wasu al'ummar Afghanistan da ke tururuwar ficewa daga Kabul babban birnin Kasar. Wakil Kohsar AFP
Talla

Tuni dakarun Taliban suka bazu a sassan birnin na Kabul lamarin da ya firgita jama’a yayinda wasu ke kokarin tserewa don tsira daga mulkin mayakan kungiyar ta ‘yan ta’adda, ko da ya ke dakarun wasu kasashe ciki har da Amurka sun isa birnin don kwashe jama’arsu.

Yanzu haka filin jirgin saman birnin na Kabul ya cika makil inda ake ci gaba da yiwa jirgi lodin da ya wuce kima saboda yawan mutanen da ke son ficewa, bayan da tun a yammacin jiya shugaba Ashraf Ghani ya fice daga kasar inda a yau ya tabbatar da nasarar Taliban ta kwace kasar.

Kwace birnin na Kabul da kuma wasu manyan yankuna cikin kwanaki 10 da Taliban ta yi na zuwa bayan kammala ficewar Sojin Amurka da ke taimakawa dakarun kasar a yaki da kungiyar lamarin da kuma ya kawo karshen yakin shekaru 20 da kungiyar ta shafe ta na yi da sojin kasar baya ga na hadakar kasashen waje da NATO.

Tuni dakarun Taliban suka kwace iko da ilahirin shingayen bincike da sauran sassan tsaro na birnin ko da ya ke sun karbe kasar ba tare da zubar da jinin da aka yi hasashe ba.

Duk da cewa Taliban da bukaci jama’ar kasar da su kwantar da hankulansu baya ga shan alwashin kin daukar fansa kan duk wani jami’I da a baya ya taimakawa gwamnati ko dakarun kasashen ketare a kokarin yakarta, har yanzu jama’a na ci gaba da tururuwa don gujewa mulkin kungiyar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ma’assasin kungiyar ta Taliban Abdul Ghani Baradar ya bukaci mayakan kungiyar da kada su kaucewa dokoki da ka’idojin da suke kai bayan kwace birnin na Kabul, musamman kan al'amuran da suka shafe take hakkin jama'a ko kuma nuna karfi kan jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.