Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Taliban ta fara taimakawa baki wajen ficewa daga Afghanistan

Taliban ta sha alwashin bai wa ilahirin bakin da ke cikin Afghanistan damar ficewa daga kasar cikin salama, matakin da ya bai wa Amurka damar ci gaba da aikin kwace al’ummarta a bangare guda mayakan kungiyar suka taimaka wajen rakiyar wasu tarin Indiyawa zuwa filin jirgi don ficewa daga kasar.

Wasu jami'an Diflomasiyyar Italiya da ke kokarin ficewa daga Afghanistan bisa rakiyar mayakan Taliban.
Wasu jami'an Diflomasiyyar Italiya da ke kokarin ficewa daga Afghanistan bisa rakiyar mayakan Taliban. STR AFP
Talla

Zuwa yanzu Amurkawa dubu 3 da 200 jiragen Soji 13 suka yi nasarar kwashewa daga Afghanistan ko da ya ke Pentagon ta ce akwai sauran ‘yan kasar kusan dubu 11 a Kabul wanda su ke kokarin kammala kwashewa kafin nan da ranar 31 ga watan Agusta wato ranar da wa’adin kammala ficewar Sojin Amurka za ta cika.

Itama India ta yi nasarar kwashe ‘yan kasarta galibinsu jami’an Diflomasiyya da ke ofishinta a birnin Kabul, aikin kwashewar da ya gudana tsakaddare bisa taimakon mayakan na Taliban, duk da takun sakar da ke tsakanin kasar da kungiyar bayan cikakken goyon bayan India ga gwamnatin Afghanistan da kuma caccakar Taliban da ma Pakistan da ke matsayin babbar mai goya mata baya.

Haka zalika mayakan na Taliban da kansu suka yiwa tawagar jami'an Diflomasiyyar Italiya rakiya zuwa filin jirgi don barin kasar.

Yanzu haka dai Taliban na da cikakken goyon bayan wasu manyan kasashe ciki har da China da Rasha baya ga Pakistan yayinda kasashen Turkiya da Amurka suka sanar da cewa za su jira kamun ludayin shugabancin kungiyar gabanin sanin alakar da za ta kasance a tsakaninsu. 

A wani taron manema labarai karon farko da Taliban ta gudanar yammacin jiya Talata, kungiyar ta sha alwashin shigar da sabbin tsare-tsare cikin shugabancinta, wanda zai sha bam bam da irin jagorancinta a shekarun 1996 zuwa 2001 da aka kifar da gwamnatinta, inda kakakinta Zabihulla Mujahid ke cewa a wannan karon shugabancin kungiyar zai tabbatar da kare hakkin dan adam musamman mata da kananan yara.

A cewar Mujahid, Taliban ba za ta nemi fansa daga kowa ba, kuma za su bai wa Mata damar karatu da kuma yin aikin gwamnati amma bisa tanade-tanaden addinin Islama.

Sai dai duk da kiraye-kirayen Taliban da kuma fara daidaituwar al’amura musamman a birnin Kabul, har yanzu wasu ‘yan kasar na kokarin ficewa don gujewa ukubar kungiyar wadda ta yi kaurin suna wajen kisa ga masu aikata laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.