Isa ga babban shafi
Taliban

Taliban na farautar mutanen da suka yi aiki da dakarun Amurka da NATO

A yayin da al’amuran yau da kullum ke neman dawo sannu a hankali a kasar Afghanistan tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe mulki, wasu bayanin sirri na Majalisar Dinkin Duniya na cewa mayakan na Taliban na bin gida-gida suna neman abokan hamayya da danginsu, lamarin da sake kara fargaba duk da ikirarin shugabannin kungiyar na afuwar bai-daya ga ‘yan kasar.

Mayakan Taliban a birnin Herat dake Yammacin Afgnaistan.
Mayakan Taliban a birnin Herat dake Yammacin Afgnaistan. AREF KARIMI AFP
Talla

Tun bayan fatattakar sojojin gwamnati da karbe iko da babban birnin Kabul a ranar Lahadin da ta gabata wanda ya kawo karshen yakin shekaru ashirin ana gwabzawa a Afghanitan, shugabannin kungiyar Taliban sun sha alwashin cikakken afuwa ga daukacin ‘yan kasar da suke ganin sun saba musu.

Bugu da kari ma sun kuma bai wa mata tabbacin cewa za a mutunta hakkokinsu, ta kowane fanni, tare da tafiyar da kasar ta wata tsarin da ya banbanta da Taliban din da ta mulkin kasar tsakanin shekarun 1996-2001.

To sai dai kamar murna ne ke neman komawa ciki ga wadanda sukaji wannan hudubar suka saki jiki. A dai-dai lokacin da dubban mutane har yanzu na ci gaba da ƙoƙarin tserewa daga birnin Kaboul, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar karin fargaba da tashin hankali.

Fargaba

Rahotan na sirri da kamfanin dillancin labarai na AFP ya leka, na nuna cewa mayakan na Taliban na bin gida-gida suna laluben mutanen da suka yi aiki da sojojin Amurka da na NATO. Rahoton wanda kuma cibiyar bincike ta kasar Norway ta rubuta, ya ce mayakan na kuma tantance mutanen da ke wucewa filin jiragen saman Kabul.

Shugabar cibiyar, Chiritian Nellemen tace Taliban na kai hari ga iyalan wadanda suka ki mika kai, da kuma gurfanar da su da hukunta iyalansu 'bisa ga tsarin shari'ar musulunci.

"Muna tsammanin duka mutanen da a baya suka yi aiki da sojojin NATO/Amurka da kawayensu, tare da danginsu za su fuskanci azabtarwa da kisa."

 

Kafar yada labarai ta Jamus Deutsche Welle ita ma ta tabbatar da cewa mayakan Taliban sun harbe dan uwan ​​daya daga cikin' yan jaridar ta yayin da suke neman sa ruwa a jallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.