Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Akwai yiwuwar kara kai hari filin jiragen saman Kabul-Amurka

Gwamnatin Amurka ta ce, akwai fargabar samun karin hare-haren a filin jirgin saman Kabul yayin da sojojin Amurkan ke gab da kammala ficewa daga Afghanistan bayan shekaru 20 suna yaki.

Yadda ake kwashe jama'ar da ke cikin hadari daga Afghanistan.
Yadda ake kwashe jama'ar da ke cikin hadari daga Afghanistan. AP - MSgt. Donald R. Allen
Talla

A makon da ya wuce ne kungiyar masu da’awar jihadi ta IS ta dauki alhakin kaddamar da harin filin jirgin saman na Kabul, a dai-dai lokacin da ake ci gaba da kwashe daruruwan ‘yan kasar da ke kokarin ficewa bayan da ‘yan tawayen Taliban suka kwace mulki.

Kakakin gwamnatin Amurka John Kirby ya ce aikin kwashe mutane a filin jirgin saman, wanda a halin yanzu dubban sojojin Amurka ke iko da shi, yana cikin hatsari, bayan kungiyar IS ta harba rokoki biyar da safiyar Litinin.

Harin da mayakan suka kai a makon jiya, ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Amurka 13, bayan kashe sama da fararen hula 100.

A cewar mai magana da yawun gwamnatin Amurka, dakarunsu suna cikin wani mummunan yanayi a yanzu, don haka suna bukatar daukar matrakan gaggawa.

Ko a karshen makon da ya wuce sai da Amurkan ta lalata wata mota da ke makare da abubuwan fashewa ta hanyar amafani da wani jirgi mara matuki, wanda take zargin mayakan ne suka shirya kai wa Amurkawa hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.