Isa ga babban shafi
Aghanistan - Taliban

Kasashen duniya na maida martani kan sabuwar gwamnatin Taliban

A yayin da Taliban ta kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan, kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani, inda Tarayyar Turai ke kashedin cewa kungiyar Taliban ba ta yi la’akari da bambamce bambamcen da ke tsakanin al’ummar kasar wajen kafa gwamnatin kamar yadda ta yi alkawari ba.

Wasu mayakan Taliban a wasu tsaunukan kasar Afghanistan.
Wasu mayakan Taliban a wasu tsaunukan kasar Afghanistan. Ahmad SAHEL ARMAN AFP
Talla

Tarayyar Turai ta ce nazarin da ta yi a kan sunayen wadanda Taliban ta bai wa manyan makaman gwamnati ya nuna cewa kungiyar ba ta cika alkawarin da ta yin a kafa gwamnatin da ya kunshi dukkannin bangarorin kasar ba.

Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid lokacin taron manema labarai na farko bayan kwace mulki a Kabul, 17/08/21.
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid lokacin taron manema labarai na farko bayan kwace mulki a Kabul, 17/08/21. AP - Rahmat Gul

Kasashe 27 na kungiya Tarayyar Turai sun gindaya sharruda biyar da cika su zai yaukaka dasawarsu da Taliban, ciki har da kafa gwamnatin wucin gadi da za ta wakilci ilahirin al’ummar kasar.

Tuni dai sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fara tattaunawa da wasu kasashen duniya dangane da makomar Afghanistan, inda ya gana da ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, gabanin taron kasashen G20 a kan kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken lokacin ganawa da Matan Afghanistan dake Qatar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken lokacin ganawa da Matan Afghanistan dake Qatar. Olivier DOULIERY POOL/AFP

Ita ko China, na’am ta yi da kawo karshen  makonni 3 na tabarbarewar doka da oda a Afghanistan sakamakon kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya, tana mai kira ga Taliban ta maido da kasar cikin hayyacinta.

A ranar Talatar nan ne Taliban ta kaddamar da gwamnatin rikon kwarya wadda babu mata ko wadanda ba ‘yan kungiyar ba, kuma ta kunshi jami’anta da ke karkashin takunkuman majalisar dinkin  duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.