Isa ga babban shafi
Lebanon

Taron tallafa wa Lebanon ya tara fiye da abin da ake bukata

Taron masu ba da gudummawa na kasa da kasa da ya gudana a ranar Laraba, ya tara miliyoyin daloli domin bai wa Lebanan taimakon gaggawa, wanda kuma tuni Faransa da ta jagoranci taron ta sanar da cewa kudaden da aka tara sun zarce adadin da aka sha alwashin samu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, a yayin bude taron kasa da kasa na 3 kan Lebanon.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, a yayin bude taron kasa da kasa na 3 kan Lebanon. AFP - CHRISTOPHE SIMON
Talla

Tun da fari dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi niyyar jagorantar tara akalla dala miliyan 350 na agajin gaggawa ga al’ummar Lebanon da ke cikin halin kaka-ni-ka-yi.

A karshen taron da ya gudana a jiya Laraba, adadin kudaden da kasashen duniya akalla 40 gami da manyan hukumomi suka alkawarta bai wa Lebanan ya kai dala miliyan 370.

Taron ya gudana ne bayan cika shekara guda da fuskantar iftila’in fashewar sinadaran Amonium da aka adana a babbar tashar ruwan kasar da ke Beirut lamarin da ya kai ga ragargajewar kusan rabin babban birnin kasar ta Lebanon bayan da lakume rayukan mutane fiye da 200 da kuma jikkata wasu dubbai.

Iftila’in da ya auku a ranar 4 ga watan Agustan shekarar 2020, ya kara tagayyara tattalin arzikin Lebanan, wanda dama ke cikin mawuyacin hali.

Bayanai daga Lebanan na cewa al’ummar kasar na fama da karancin kayayyakin abinci da man fetur, da kuma magunguna, matsalolin da suke karuwa sakamakon gaza kafa karbabbiyar gwamnatin hadin gwiwa, saboda rikicin siyasar da kasar ta Lebanan ke ciki.

Sasanta rikicin siyasar Lebanan dai shi ne babban sharadin da kasashen duniya gami da manyan hukumomi suka gindaya wa kasar kafin mika mata makudan kudade a matsayin tallafi.

Dimbim mutane ne suka fito zanga zanga a sassan kasar, a deaidai lokacin da ake cika shekara daya da fashewar sinadarai tashar jiragen ruwan Lebanon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.