Isa ga babban shafi
Lebanon-MDD

Majalisar Dinkin Duniya da Faransa sun sha alwashin agazawa Lebanon

Faransa da Majalisar Dinkin Duniya sun lashi takobin ci gaba da samar da kayayyakin agaji ga Lebanon, amma sun bukaci jagororin kasar da su kafa sabuwar gwamnati, ganin yadda tankiyar siyasa ta hana kasar samun agajin biliyoyin Dala a dai dai lokacin da take fama da tarin rikice-rikice.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. RFI
Talla

Taron da Majalisar Dinkin Duniya da Faransa suka shirya kan agazawa Lebanon, shi ne karo na biyu tun bayan da kasar ta gamu da ibtila’in fashewar sinadarai a tashar jiragen ruwan birnin Beirut, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 200, yayin da dubbai suka jikkata baya ga kadarori da suka lalace.

Ibtila’in fashewar ya auku ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar karancin kudi a asusunta saboda annobar coronavirus wadda ta haddasa tsadar kayayyaki da talauci da kuma zaman kashe-wando.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, sun sanar da kafa wata gidauniya karkashin Bankin Duniya da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai domin samar wa Lebanon da tallafi, ciki har da abinci da lafiya da ilimi da kuma sake gina tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut.

A yayin gabatar da jawabinsa, Guterres ya ce, za su iya agaza wa al’ummar Lebanon don ceto su daga halin da suka tsinci kansu a ciki.

Shi kuwa Macron cewa ya yi, taron na jiya Laraba zai bada damar kammala daukin gaggawa tare da samnar da agaji cikin hanzari ga Lebanon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.