Isa ga babban shafi
Faransa -Lebanon

Shugaba Macron zai gana da manema labarai gobe lahadi kan halin da ake ciki a Lebanon

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da manema labarai gobe lahadi kan halin da ake ciki dangane da siyasar Lebanon bayan da Firaministan kasar ya sauka daga mukamin sa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Fadar shugaban Faransa tace shugaba Macron wanda sau biyu yana zuwa Lebanon tun bayan hadarin da aka samu a tashar jiragen ruwan kasar wanda yayi sanadiyar rasa rayuka, na bukatar ganin an kafa sabuwar gwamnatin da zata aiwatar da sauye sauyen da jama’ar kasar ke bukata.

Macron ya jagoranci kaddamar da gidauniyar da ta Tarawa Lebanon agajin kudade, amma al’ummar kasar sun bukaci jinkirta baiwa shugabannin kasar kudaden har sai an samu sabuwar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.