Isa ga babban shafi
Lebanon - Tattalin Arziki

Faduwar darajar kudin Lebanon ya janyo bore biranen Tripoli da Beirut

Daruruwan masu zanga-zanga a Lebanon sun yi yunkurin kutsawa cikin gine-ginen babban bankin kasar a jiya Asabar, bayan da kafafen yada labarai suka ruwaito faduwa mafi muni da darajar kudin kasar ta Lebanon yayi cikin shekaru fiye da 22.

Masu zanga-zanga a birnin Beirut na kasar Lebanon kan lalacewar tattalin arziki kasar.
Masu zanga-zanga a birnin Beirut na kasar Lebanon kan lalacewar tattalin arziki kasar. © ANWAR AMRO / AFP
Talla

Yanzu haka dai kudin Lebanon na Pound dubu 1 da 507 ne ke daidai da dalar Amurka 1, abinda ke zama koma bayan tattalin arziki mafi muni da kasar ta gani tun bayan wanda aka gani a shekarar 1997.

A jiya Asabar wasu masu canjin bayan fage a kasar ta Lebanon suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, kudin kasar ta su na Pound dubu 17 da 300 zuwa dubu 17 da 500 ne ke daidai da dala 1.

Rahotanni sun ce masu zanga-zanga Beirut da Tripoli sun kokarin afkawa gine-ginen babban bankin Lebanon, gami gidajen wasu ‘yan majalisar kasar, sai dai jami’an tsaro sun dakile shirin nasu.

Tun cikin shekarar 2019, tattalin arzikin Lebanon ya shiga tsaka mai wuya, kamar yadda bankin Bankin Duniya ya bayyana.

Har yanzu dai babu cikakkiyar gwamnati a Lebanon sakamakon rikicin siyasar da kasar ke fama da shi kusan shekaru 2 a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.