Isa ga babban shafi

Bankin Duniya ya tallafawa kasashen Tafkin Chadi da dala biyan daya

Bankin Duniya ya bada dala biliyan daya domin inganta rayuwar al'ummar kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da rikici ya shafa.

Bankin duniya ya tallafawa kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da dala dubu daya.
Bankin duniya ya tallafawa kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da dala dubu daya. wikipédia
Talla

Shugaban bankin da ke kasar Chadi Rasit Pertesv ne ya bayyana hakan, ya yin taron kungiyar gwamnonin yankin karo na hudu da ya gudana a birnin N’Djamena na kasar Chadi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, taron ya zo ne a a dai-dai lokacin da ake fuskantar kalubalen tabarbarer lamura a dukkanin kasashe hudun da ke yankin, da suka hada da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar da kuma Najeriya.

Ya ce kudaden da aka fitar don rabawa tsakanin kasashen, sun taimaka wajen farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummar da suka yi fama da tashe-tashen hankula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.