Isa ga babban shafi

Ba za mu bar tsibirin Tafkin Chadi ko daya a hannun 'yan ta'adda ba - MNJTF

Kwamandan rundunar sojin hadin gwiwar da ke yaki da 'yann ta'adda a yankin tafkin Chadi ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chinuisi, yabayyana aniyarsa ta ganin sun murkushe duk mayakan Boko Haram da na ISWAP da ke zama a tsibiran da suke kewaye da tafkin baki daya.

Kwamandan rundunar sojin hadin gwiwar da ke yaki da 'yann ta'adda a yankin tafkin Chadi ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chinuisi tare da dakarunsa.
Kwamandan rundunar sojin hadin gwiwar da ke yaki da 'yann ta'adda a yankin tafkin Chadi ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chinuisi tare da dakarunsa. © RFI/Hausa
Talla

Janar Chinuisi ya bayyana haka ne, lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a Balangoua da ke kasar Kamaru, da kuma Bagasola da Bibi da ke cikin kasar Chadi a ranar Juma'ar da ta gabata.

MNJTF
MNJTF © RFI/Hausa

Babban jami'in hulda da jama'a na rundunar ta MNJTF, laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya ce Kwamandan ya bayyana karara cewar, ya  kai ziyarar ce domin tantance karfin rundunonin da ke bakin aiki daga da kuma karfafa musu guiwa wajen ganin sun cigaba da jajircewa a yakin da suke gwabzawa, yayin da ya yi musu alkawarin taimakon da suke bukata domin samun nasara.

Kanal Abdullahi ya ce kafa rundunar MNJTF ta taka rawa gaya wajen dakile kaifin mayakan Boko Haram wajen shirya kai hari a tsibiran da ke Tafkin Chadi da ake kira Tumbus, yayin da janar Chibuisi ya bukaci sojojin da suk dada kara kaimi wajen dorawa akan nasarorin da suka samu, domin kawar da mayakan daga tsibirin.

Kwamandan rundunar sojin hadin gwiwar da ke yaki da 'yann ta'adda a yankin tafkin Chadi ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chinuisi a lokacin da ya ke sauka daga jirgin ruwan sojoji a yankin tafkin Chadi
Kwamandan rundunar sojin hadin gwiwar da ke yaki da 'yann ta'adda a yankin tafkin Chadi ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chinuisi a lokacin da ya ke sauka daga jirgin ruwan sojoji a yankin tafkin Chadi © RFI/Hausa

Ziyarar aikin ta Kamaru da Chadi na zuwa ne kwana guda bayan kammala irinta da Kwamandan ya kai Malam Fatori da ke Najeriya da kuma Diffa da Bosso a Jamhuriyar Nijar, a kokarin da sojojin ke yi na kawar da ayyukan ta'adddanci a yankin Tafkin Chadi baki daya domin mayar da zaman lafiya..

Kanal Abdullahi ya ce Janar Chibuisi ya sha alwashin bai wa dakarun goyon bayan da suke bukata domin samun nasarar yakin baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.