Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar miliyoyin 'yan Najeriya su tsunduma cikin talauci - Bankin Duniya

Bankin Duniya ya gargadi gwamnatin Najeriya kan yiwuwar samun karin ‘yan kasar miliyan 7.1 da za su fada cikin kangin talauci, muddin ba ta dauki matakan sassauta wa ‘yan kasar kuncin da suka shiga ba, saboda cire tallafin man fetur. 

Birnin Lagos mai cike da hada-hadar al'umma a kullum.
Birnin Lagos mai cike da hada-hadar al'umma a kullum. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

 

Cikin rahoton da ya fitar a farkon makon nan, bankin duniyar ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta yi amfani da wani kaso na makudan kudaden da za ta alkinta sakamakon soke shirin tallafin mai, wajen rage wa ‘yan kasar radadin da suke ciki a dalilin garambawul din da ta yi wa tsarin tattalin arzikinta. 

Tun da fari dai Bankin Duniyar ya ce Najeriya za ta iya alkinta kudin da yawansu ya kai naira tiriliyan 3 da biliyan 900 a shekarar bana kadai, sakamakon garambawul din da gwamnati ta yi na soke shirin tallafin man fetur, wanda kididdiga ta nuna cewar a shekarar bara kadai sai da ya lakume wa gwamnati dala biliyan 10.  

Makwanni kadan bayan cire tallafin man ne kuma, gwamnatin Najeriyar ta mayar da tsarin canjin kudaden kasashen ketare zuwa na bai daya, abinda ya sanya darajar dalar Amurka guda haura naira 700. 

Sai dai a yayin da bankin duniyar ya yaba da matakan da Najeriya ta dauka, ya yi gargadin cewar al’ummmar kasar za su yi fama da hauhawar farashin kayayyaki, kalubalen da ya ce na takaitaccen lokaci ne, domin al’amura za su daidaita zuwa nan gaba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.