Ana Zanga-zangar kyamar Trump a Amurka
Daruruwan mutane sun shiga zanga zangar adawa da zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump a sassa daban-daban na kasar, inda suka sha alwashin ci gaba da adawa da manufofin sa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A birnin Washington daruruwan masu zanga zangar suka taru a gaban fadar shugaban kasa, duk da sanyin da ake yi, inda suka bayyana Trump a matsayin mai nuna banbancin launin fata da cin zarafin mata da kuma raba kan al’umma.
A birnin New York, masu zanga zangar sun kona tayun mota a Dandalin hadin kai, a Carlifornia daliban makarantu ne suka fice daga azuzuwa dan adawa da shugaban, a Los Angeles daruruwan matasa suka gudanar da gangami a Dakin taron birnin suna cewa su Trump fa ba shugaban su bane.
A Pennsylvania, daruruwan daliban jami’ar Pittsburg suka yi jerin gwano a titunan birnin, a Carlifornia kuma an raunana daya daga cikin masu zanga zangar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu