Isa ga babban shafi
Amurka

Republican ke da rinjaye a Majalisar wakilai da Dattijai

Jam’iyyar Republican ta lashe zaben majalisar Wakilai tare da haramtawa Democrat karbe ragamar majalisar Wakilai a zaben Amurka da aka gudanar inda dan takarar Jam’iyyar Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasa.

Jam'iyyar Republican ta samu rinjaye a Majalisar Dattijai da wakilai a zaben Amurka
Jam'iyyar Republican ta samu rinjaye a Majalisar Dattijai da wakilai a zaben Amurka REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Republican ta samu rinjayen kujerun Majalisar Dattijai 54, yayin da 46 suka fada hannun ‘Yan Democrat.

A cikin sanarwar da ya fitar Shugaban Republican Reince Priebus ya ce wannan babbar nasara ce ga Jam’iyyar bayan sun lashe kujerar shugaban kasa tare da ci gaba da rike ragamar Majalisar Dattijai.

Republican ta samu kujeru 239 a Majalisar Wakilai wanda ya ba Jam’iyyar ci gaba da jagoranci a Majalisar na tsawon shekaru shida. Democrat ta samu kujeru 196 ne a zaben.

Sakamakon zaben dai ya sabawa kuri’un jin ra’ayoyin jama’a da dama da kafofin yada labarai suka gudanar.

Rashin lashe Majalisar Dattijai dai baraka ce ga Democrat musamman wajen kokarin toshe wasu sabbin tsare tsaren shugaban kasa Donald Trump.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.