Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya lashe zaben Amurka

Dan takarar Republican Donald Trump ya lashe zaben sugaban kasar Amurka bayan ya doke abokiyar hamayyar shi Hillary Clinton ta Democrat. Sabon shugaban ya yi alkawalin zama shugaba ga Amurkawa.

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump
Zababben Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Mike Segar
Talla

Trump ya samu kuri’un wakilai 278 daga cikin 270 da ya ke bukata domin lashe zaben na Amurka, yayin da Hillary Clinton ta samu kuri’u 219.

A lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayan shi, Donald Trump ya jinjinawa abokiyar hamayyar shi Hillary Clinton wacce tuni ta kira shi ta amsa shan kaye.

Sai dai kuma nasarar da Trump ya samu ta sa darajar dala da kasuwannin hannayen jari a duniya sun fadi, sannan darajar kudin Mexico ta yi faduwar da ba a taba gani ba.

Akasarin kasuwannin sun yi fatar ganin Hillary Clinton ta samu nasara, amma yadda sakamakon ya kasance Trump ne akan gaba ya jefa shakku da fargaba tsakanin ‘Yan kasuwa a duniya.

Masu ra’ayin rikau irin na Trump daga kasashen Turai irinsu Marine Le Pen a Faransa sun fara aiko ma shi da sakon taya murna.

Trump dai na da manufofi da halaye da ke razana duniya musamman kyamar musulmi da baki da kuma manufofin tattalin arziki da diflomasiyar duniya.

A ranar 20 ga watan Janairu ne Donald Trump zai shiga fadar White House a matsayin sabon shugaban Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.