Isa ga babban shafi
US

Shugabanni Afrika sun ta ya Trump murna

Shugabannin Kasashen Afrika na ci gaba da aike sakon ta ya murna ga Donald trump sakamakon nasarar da ya samu, da kuma fatar yin aiki tare.

Zababben Shugaban Kasar Amurka Donald Trump
Zababben Shugaban Kasar Amurka Donald Trump REUTERS/Mike Segar
Talla

Cikin shugabannin da suka bayyana sakwannin nasu sun hada da Uhuru Kenyatta na Kenya, da Jacob Zuma na Afirka ta kudu da Muhammadu Buhari na Najeriya.

Shi kuma Shugaban Masar Abel Fata al-sisi fatan ganin sabon shugaban Amurkan ya taka rawar dawo da zaman lafiya a gabas ta tsakiya ya yi, bayan taya shi murna, a daidai lokacin da Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana Trump a matsayin abokin tafiya na gaskiya wajen sake karfafa Isra’ila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.