Isa ga babban shafi
Yemen

Bam Ya Kashe Sojan Yemen 3

Sojan kasar Yemen uku suka gamu da ajalinsu yau asabar a lokacin da wani kunshin Bam da suka kwanshe suka saka cikin motar su ya tarwatse a kusa da wata kasuwa.

Wani barna da hare-haren masu jihadi ya haifar a kasar Yemen kwanan baya
Wani barna da hare-haren masu jihadi ya haifar a kasar Yemen kwanan baya REUTERS/Fawaz Salman
Talla

Wasu mutanen bakwai da suka hada da fararen hula uku suka jikkata a sakamakon tsautsayin da ya auku a garin Huta babban birnin Gunduman Lahj wanda yayi kaurin suna a matsayin dandalin kurdawa masu jihadi.

Ana zargin masu ikirarin jihadi suka dasa bam din da sojan suka dauka cikin motar su bayan sun zaci sun kashe karfin sa.

Sojan da suke goyon bayan Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi dake samun taimakon sojan kasar Saudiyya na fafatawa da masu ikirarin jihadi ne da kuma mayakan Shia na Huthi dake rike da wurare da dama a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.