Isa ga babban shafi
Yemen

An samu tsaiku a tattaunawar Yemen

An samu tseko wajen fara taron sulhunta bangarorin kasar Yemen da ke yaki da juna, saboda rashin halartar wakilan ‘yan tawaye a zauren taron da ake gudanarwa a kasar Kuwait.

Abd Rabbo Mansour Hadi na Yemen
Abd Rabbo Mansour Hadi na Yemen AFP/Archives
Talla

Babbar manufar taron wanda Majalisar Dinkin Duniya ke da masaniya a kai, ita ce kokarin samar da mafita ga rikicin da ya share tsawon watanni 13 ana yi tare da hasarar rayukan dubban mutane.

Rashin halatar ‘yan adawar a ranar farko ya sa an soma nuna shakku a game da makomar taron.

Yanzu haka dai wakilan gwamnatin Yemen sun isa Kuwait.

A makon jiya bangaren gwamnatin shugaba Abedrabbo Mansour Hadi da bangaren ‘Yan tawayen Huthi yan shi’a da suka kore shi daga fadar shi a Sanaa dukkaninsu sun yi alkawalin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma Saudiya da kawayenta da ke luguden wuta akan ‘yan tawaye sun amince su dakatar da kai hare hare karkashin yarjeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta.

Sai dai bangarorin dukkaninsu sun sabawa yarjejeniyar tsagaita wutar tare da zargin junansu.

Wata majiya daga bangaren ‘Yan tawayen ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa sun ki halartar taron ne a Kuwait saboda hare haren da Saudiya ke ci gaba da kai wa akan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.