Isa ga babban shafi
Yemen

Za a mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a Yemen

Bangarorin da ke fada da juna a Yemen sun lashi takobin mutunta yarjejeniyar tsagaita musayar wuta wadda ta fara aiki da misalin karfe 12 na daren da ya gabata.

Masu fada da juna a Yemen sun yi alkawarin mutunta yarjejeniyar tsagaita musayar wuta.
Masu fada da juna a Yemen sun yi alkawarin mutunta yarjejeniyar tsagaita musayar wuta. REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

 

Ana sa ran aiki da yarjejeniyar wadda ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya, zai kai ga sabuwar tattaunawar zaman lafiyan na din din a kasar.

Babban hafsan dakarun da ke goyon bayan shugaba Abedrabbo Rabuh Mansur Hadi, Janar Mohamed Ali al-Makdashi ya fada wa maneman labarai cewa, za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar har sai mayakan Houthi sun karya ta.

A baya can, sau uku yunkurin tsagaita wuta a Yemen ya tabarbare yayin da Saudiya ta fara jagorantar hare haren sama a bara, a wani mataki na mara wa gwamnatin kasar baya tare da fatattakar mayakan Houthi da suka mamaye babban birnin Sanaa a watan Satumban shekarar 2014.

Rikicin Yemen dai ya yi sanadiyar mutuwar dubban jama’a yayin da kimanin miliyan 2.4 suka rasa muhallansu .

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.