Isa ga babban shafi
Yemen

An kashe fararen hula 41 a harin Yemen

Majiyoyin kiwon lafiya a kasar Yemen sun tabbatar da mutuwar mutane 41 dukkaninsu fararen hula, sakamakon hare-hare ta sama da sojojin kawance a karkashin jagorancin Saudiya suka kai a kan wata kasuwa da ke lardin Hajja na arewacin kasar.

Jiragen yakin Saudiya da kawayenta na ci gaba da luguden wuta akan 'Yan Huthi a Yemen
Jiragen yakin Saudiya da kawayenta na ci gaba da luguden wuta akan 'Yan Huthi a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Wani babban jami’i a kungiyar Likitoci ta kasa da kasa wato Medecins Sans Frontieres, ya ce yanzu haka akwai gawarwakin mutanen 41 da kuma wasu mutane 35 da suka samu raunuka da aka ajiye a asibitin da kungiyar ta kafa a yankin da lamarin ya faru.

Wani jami’in kiwon lafiyar na daban, ya tabbatar wa manema labarai cewa dukkanin mamatan fararen hula ne da suka hada da kananan yara.

Shugabannin kabilu a lardin na Hajja, sun ce jiragen yakin, sun kai hare-haren da manyan bama-bamai akalla sau biyu akan kasuwar garin Mustaba’a, daya daya cikin garuruwan da ke karkashin kulawar ‘yan tawayen Hutsi.

A cikin watan da ya gabata, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rigths Watch, ta zargin sojojin kawancen da harba bama-baman da aka haramta yin amfani da su a duniya, yayin da wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ke cewa sojojin na kawance, sun kai hare-hare akan fararen hula a lokuta daban daban har sau 119 a kasar ta Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.