MSF ta la’anci harin da aka kai a wata asibiti a Yemen
Kungiyar Agaji ta Medicins Sans Frontier ta yi allawadai da harin da aka kai wani asibiti a kasar Yemen wanda ya hallaka mutane 4.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da kungiyar ta bayar ta ce mutane 4 suka mutu sannan wasu 10 suka jikkata sakamakon harin da aka kai da makami mai linzami.
Kungiyar tace an kai harin ne a asibitin da k karkashin kulawarta a Razeh da ke Yankin Saada, kuma tuni aka kwashe ma’aikatan da ke ciki da masu jinya zuwa wasu asibitocin don kula da su.
Daraktan kungiyar Raguel Ayora ya ce ya zuwa yanzu ba za su iya cewar ko harin da Saudi Arabia ke kai wa ne ya samu asibitin ba ko kuma ‘yan tawaye ne suka harba makamin roka.
Jami’in ya ce akai-akai suna sanar da bangarorin da ke rikici a kasar ayyukan agajin da suke yi don ceto rayukan jama’a.
Saudiya da kawayenta dai na ci gaba da kai farmaki ta sama akan mayakan Huthi ‘Yan Shi’a da ke fada da gwamnatin Yemen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu