Isa ga babban shafi
Yemen

Amurka ke Siyarwa Saudiya bama-bamai da ta ke kai hari Yemen

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watc, ta ce bama-baman da Amurka ke siyarwa rundunar hadakar kasashen larabawa da kasar Saudiya ke jagoranta, da shi akayi amfani wajen kai harin sama da ya yi sanadiyar kashe fararen hula 97 a Yemen.

Human Rights Watch
Human Rights Watch © Reuters
Talla

Hare-hare 2 da aka kai kan kasuwar da ke cike da jama’a a garin Mastaba arewa maso yammacin kasar Yemen, a ranar 15 ga watan maris da ya gabata, ya yi sanadiyar kashe ‘yan tawayen huthi da 'yan shi’a da dama.

Kungiyar HRW ta ce wannan na a matsayin laifukan yaki ne, da ya kamata duniya ta yi hukunci a kai, inda ta bukaci Amurka da ta daina siyarwa Saudiya da makamai.

Zargin HRW dai ya zo ne a kan gaba, dai-dai wani lokaci da sakataren harakokin wajen kasar Amurka John Kerry ya fara wata ziyara a yankin Golf, inda maganar yakin kasar Yemen za ta taso.

HRW ta ce bincikenta na ranar 28 ga watan maris inda lamarin ya faru, ta gano sauran tarkacen bama-baman samfarin GBU 31, da tauraron dan Adam ke sarrafawa da kuma samfarin MK 84, dake da nauyin kilo 907 da kasar Amurka ta kera.

Kungiyar ta kuma bayyana Saudiya a matsayin kasar da ke aikata kisan rashin imani kan fararen hulan kasar Yamen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.