Isa ga babban shafi
Yemen

HRW : ‘Yan tawayen Yemen sun aikata laifun yaki

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi ‘Yan tawayen Huthi da ke fada da gwamnatin kasar da aikata laifukan yaki tare da yin kira ga bangarorin da ke rikici su kare rayukan fararen hula.

REUTERS
Talla

A cikin rahoton da Kungiyar ta fitar, ta ce ‘Yan tawayen sun harbi mata guda biyu a kudancin birnin Aden a watan jiya tare da kame wasu ma’akatan agaji guda 10 a makwanni biyu da suka gaba.

Daraktan kungiyar Joe Stork da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika ya ce suna fargabar an aikata laifukan yaki da dama a rikicin Yemen duk da akwai tarnaki wajen shiga kasar domin gudanar da bincike.

Yanzu haka ‘Yan Tawayen Yemen sun yi nasarar kutsa kai Yankin Tawahi da ke Aden duk da luguden wuta da Saudiya ke yi da jiragen yaki a sansaninsu

Rahotanni sun ce akalla mutane 120 aka kashe a jiya Laraba a hare haren da Saudi ke kai wa da kuma fafatawa tsakanin mayakan Houthi ke yi da sojojin Yemen.

Mayakan Houthi da ke samun goyan bayan tsohon shugaban kasa Ali Abdallah Saleh sun kwashe makwanni suna yi wa garin Aden kawanya.

Ana sa ran Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ke ziyara Saudi Arabia ya bukaci a tsagaita wuta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.