Isa ga babban shafi
Yemen-Saudi Arabiya

Jagoran 'yan tawayen Yemen yace ba zai mika kai ba

Jogoran ‘yan tawaye na kasar Yemen Abdulmalik Al-Huthi yace ba zai bada kai ba, gameda hare-haren da kasar Saudiyya ke jagoranta ana ta kai masu. Al-Huthi yace hare haren ba wani abu bane illa kawai kutse da ake yi masu cikin kasa.Jogoran ‘yan tawayen, na Magana ne yayin wani jawabi na musamman da yayi gameda cika kwanaki 25, da ake kai masu hare-hare bisa jagorancin kasar Saudiyya.A halin da ake ciki kuma, kungiyoyin aikin agaji a Yemen din sun nuna rashin jin dadinsu gameda yadda ‘yan tawayen ke kawo cikas wajen raba kayyakin agaji ga mabukata.Duk wannan na zuwa ne yayinda tashe tashen hankula tsakanin ‘yan tawaye da dakarun gwammarti da hare haren sama da kasar Saudiyya ke jagoranta, suka yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 60.Hukumomin birnin Riyadh kuma sun yi alkawarin samar da dukkan kudaden da Majalisar Dinkin Duniya ke nema don agaza wa kasar ta Yemen.Majalisar ta Dinkin Duniya tace tana neman kudaden da suka kai dalar Amurka miliyon 274, don samar da ababen more rayuwa a kasar, 

Wasu 'yan tawayen Huthi na kasar Yemen
Wasu 'yan tawayen Huthi na kasar Yemen AFP PHOTO / MOHAMMED HUWAIS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.