Isa ga babban shafi
Yemen-Saudi Arabiya

Saudiyya zata samar da dukkan kudaden da ake bukata a Yemen

Yau Asabar kasar Saudi Arabia tayi alkawarin samar da dukkan kudaden tallafin da ake bukata, don samar da ababen more rayuwa ga al’ummar kasar Yemen. Ana bukatar kudi Dalarr Amurka Miliyon 274, don samar ababen bukata ga al’ummar kasar.Dama kasar ta Saudi Arabia ke jagorantar hare haren da ake kaiwa a kan mayakan Huthi mabiya shi’a a kasar ta Yemen.MDD tace daruruwan mutane ne suka mutu, yayinda dubunnan iyalai kuma suka tsere daga gidajensu, sakamakon yakin da ake gwabzawa, da kuma yayi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaron kasar Saudiyya 6, a kan iyakar kasar. 

Ministan harkokin wajen kasar Saudi Arabiya Saud al-Faisal
Ministan harkokin wajen kasar Saudi Arabiya Saud al-Faisal REUTERS/Faisal Al Nasser
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.