Isa ga babban shafi
Saudi-Faransa

Faransa ta goyi bayan Saudiya akan Yemen

Kasar Faransa ta bayyana nuna goyon bayanta ga hare haren jiragen sama da Saudiya ke kai wa akan ‘Yan tawayen Huthi da ke fada da gwamnatin Yemen. Saudiya ta  ce ta kai hare haren sama kimanin 1,200 tare da kashe mayakan Huthi da dama a Yemen.

Wani dan tawayen Huthi a Yemen
Wani dan tawayen Huthi a Yemen REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

An shafe tsawon makwanni uku Saudiya na yi wa mayakan Huthi ‘yan shi’a luguden wuta a Yemen. Kuma Kasar Farana ta bayyana goyon bayanta ga hare haren na Saudiya.

Ministan harakokin wajen Faransa Lauent Fabius wanda ya kai ziyara Saudiya akan batun Yemen, ya ce Faransa na goyon bayan matakan da kasashen larabawa 9 suka dauka, wanda Saudiya ke jagoranta, domin kubutar da kasar Yemen daga barazanar mayakan da suka kori gwamnati.

Fabius ya gana da Sarki Salman na Saudiya tare da bayyana cewa suna bayan kasar.

Tun a ranar 26 a watan Maris ne Saudiya ke jagorantar hare haren jiragen sama kan mayakan Huthi da suka karbe ikon Sanaa fadar gwamnatin Yemen.

Kasar Saudi Arabiya tace ‘Yan Tawayen Huthi sama da 500 ta kashe tun hare haren sama da ta kaddamar akansu a iyakokinta da kasar Yemen.

A yau Lahadi kawai, kimanin ‘Yan tawaye 15 Jiragen yakin Saudiya suka kashe a wani sansaninsu da ke kudancin birnin Aden.

Saudiya dai da kwayenta na kallon mayakan na Huthi a matsayin barazana gare su, domin yadda suke kokarin mamaye kasar Yemen da fargabar yiyuwar tsallokowa zuwa Saudiya da wasu kasashen da ke makwabtaka da Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.