Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

Jiragen yakin Saudiya sun kashe ‘yan Huthi 12 a Yemen

Jiragen yakin Dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta sun kashe ‘Yan tawayen Huthi akalla 12 a jerin hare-hare da aka yi ta kai wa sassan Yemen. Bayanai na cewa An yi wa wata makaranta da mayakan Huthi suka mayar da ita sassaninsu, raga-raga a yankin Ataq, babban birnin gunduman Abyan.

Wani Dan Huthi rike da sanarwa yana kiran a kawo karshen yaki a Yemen.
Wani Dan Huthi rike da sanarwa yana kiran a kawo karshen yaki a Yemen. REUTERS
Talla

Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin Dakarun kasar da ke biyayya ga shugaba Abdrebbo Mansur Hadi da kuma ‘Yan tawayen Huthi mabiya Shi’a da Iran ke maraewa baya, duk da matsin lamba da bangarorin biyu ke fuskanta daga kasashen duniya na ganin sun hau teburin sulhu.

‘Yan tawayen da suka karbe ikon sassan yankunan Yemen da dama, tare da tursasawa shugaba Hadi ya fice daga kasar, sun bukaci Kasar Saudiya ta dakatar da hare haren jiragen sama da ta ke kai musu kafin su amince a hau teburin tattaunawa.

Kasar Amurka da ke goyon bayan gwamnatin Yemen ta bukaci ‘yan tawayen su amince a tattauna, domin kawo karshen rikicin kasar da ya lukume rayukan mutane sama da 1,000.

Yanzu haka Majalisar Dinkin Duniya ta nada Ismail Ould Cheikh Ahmed dan kasar Mauritiania a matsayin sabon jekadanta na musamman.

Chiek Ahmad ya maye gurbin Jamal Benomar, wanda ya yi mursabus saboda zargin da wasu kasashen larabawa suka yi akan yana nuna ra’ayinsa ga ‘yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.