Isa ga babban shafi
Yemen

Iran na son a sasanta rikicin Yemen

Kasar Iran ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci taron sasanta rikicin Yemen don kawo karshen tashin hankalin da ya hallaka dimbin rayuka yanzu haka. Ministan harkokin wajen kasar Mohammed Javad Zarif ya ce ya dace dukkanin bangarorin da ke rikici a Yemen su shiga taron sasantawar ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Ministan harakokin kasar Iran Javad Zarif
Ministan harakokin kasar Iran Javad Zarif REUTERS/Caren Firouz
Talla

Iran dai ta fito tana bayyana adawa da hare haren da jiragen sama da Saudiya da kawayenta ke kai wa a Yemen.

Yanzu haka ana ci gaba da gwabza fada tsakanin Dakarun kasar da ke biyayya ga shugaba Abdrebbo Mansur Hadi da kuma ‘Yan tawayen Huthi mabiya Shi’a da Iran ke maraewa baya, duk da matsin lamba da bangarorin biyu ke fuskanta daga kasashen duniya na ganin sun hau teburin sulhu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zuwa yanzu an kasha sama da mutane 1000 daga watan Maris zuwa yanzu a rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.