Isa ga babban shafi
HRW-Amnesty-Saudiya

HRW da Amnesty sun yi kiran dakatar da hukuncin kisa da za’a yanke wa mutane 7 a Saudiya

Hukumomin kare hakkin Bil’adama, Human Rights Watch da Amnesty international sun yi kira ga mahukuntan Saudiya su dakatar da hukuncin kisa da aka shirya yanke wa wasu mutane bakwai da aka kama da laifin fashi da makami.

Sarki Abdallah na kasar Saudiya tare da Sarkin Kuwait heikh Sabah al-Ahmad al-Sabah  a taron kasashen Musulmi a birnin Makkah
Sarki Abdallah na kasar Saudiya tare da Sarkin Kuwait heikh Sabah al-Ahmad al-Sabah a taron kasashen Musulmi a birnin Makkah REUTERS
Talla

Hukumomin biyu sun ce mutanen dukkaninsu matsa ne ‘Yan shekaru tsakanin 16 zuwa 20.

HRW tace hukuncin ya yi tsauri ga laifin aikata fashi da makami a tsarin dokar Shari’a a Saudiya.

A wata Sanarwa, Mataimakin shugaban hukumar HRW da ke kula da yankin Gabas ta tsakiya, Eric Goldstein yace hukuncin zai sabawa dokokin kare hakkin bil’adama idan Saudiya ta yanke wa matasan hukunci.

Amnesty Internetional tace an gallazawa mutanen guda bakwai azaba domin su amsa laifinsu kuma hukuncin da za’a yanke ma matasan ya sabawa dokokin hukumar.

A tsarin dokar Saudiya, ana yanke hukuncin kisa ga laifukan da suka hada da fyade da kisa da fashi da makami da safarar miyagun kwayu sannan idan mutum ya yi ridda ya canza sheka daga Addinin Musulunci zuwa wani addini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.