Saudiya ta umurci ‘Yan kasar da su gujewa tarurruka a Jordan
Hukumomi a kasar Saudia sun umurci ‘Yan kasar da su gujewa halarta tarurruka da Jami’oi a yayin da bore akan tsadar mai ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya, ya kuma raunata mutane 71 a kasar ta Jordan.
Wallafawa ranar:
Ofishin Jakadancin kasar ne a Amman ya fitar da wannan sanarwa ga masu aiki a kasar ta Jordan da dalibai dake karatu a kasar.
Tashin hankali a kasar ta Jordan ya barke ne a ranar Talata bayan karin farashin gas da aka yi a kasar da kashi 53 da kuma na mai da kashi 12.
A cewar Firaministan kasar Jordan, Abdulla Nsur, karin ya zama dole domin kasar na bukatar ta tsohe gibin kasafin kudin bana na kudi Dalar Amurka biliyan 3.5. da aka samu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu