Isa ga babban shafi
Yemen

Sabon Rikici Na Neman Sukurkuta Yarjejeniyar Sulhu a Yemen

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa an sami gwabza fada tsakanin Dakarun Gwamnati da ‘yan tawaye, al'amarin da ke neman sukurkuta yarjejeniyar Tsagaita wuta da MDD ta shata.

Shugaba Adb-Rabbu Mansour Hadi na kasar Yemen
Shugaba Adb-Rabbu Mansour Hadi na kasar Yemen REUTERS/Stringer
Talla

Bayanai  na nuna cewa Dakarun dake goyon bayan Shugaban kasar Abdelrabbo Mansour Hadi sun gwabza fada da ‘Yan Shia na Huthi a gunduman Marib, Gabashi da Arewaci inda ‘yan tawaye suka ja daga a birnin Sanaa.

Bayanan na cewa tun cikin dare  Sojan Gwamnati da ‘yan tawaye suka mamaye yankin na Sarwah, dake  Marib inda suka mamaye tsaunukan yankin.

Sojan hadin guiwa da kasar Saudiyya ke jagoranta sun kaddamar da yakar ‘yan tawayen dake samun goyon bayan Iran, tun bara ake ta gwabza fada.

Daga lahadi da aka amince a tsagaita wuta ya zuwa  littini rayukan soja bakwai suka salwanta, wasu 15 kuma suka jikkata a fadace-fadacen da aka gwabza.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.