Isa ga babban shafi
Yemen

zaa soma musayar fursunoni tsakanin bangarori masu rikici da juna a Yemen

Kwana guda bayan cimma yarjejeniyar tsaigata bude wuta a kasar Yemen, a yau laraba bangarorin dake rikici da juna sun amince su fara musayar Fursunoni, wannan dai mataki ne na nuna amincewarsu da yarjejeniyar zaman lafiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Daya daga cikin mayakan Houthi
Daya daga cikin mayakan Houthi REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Zaman Sulhun da aka soma a jiya talata a Switzerland, na ci gaba duk da cewa ana ta jin karar bindigogi a cikin kasar, yayin da bangarorin biyu suka fara zargin junansu da karya dokokin Yarjejeniya.

Wani Jami’in kwamitin dake kula da harkokin Fursunoni a kasar Mokhtar al-Rabbash kuma na hannun dama a Gwamnati shugaba Abdurrabuh Mansour Hadi, ya ce an amince daga yau a fara musayar ‘yan tawayen Huthi 375 da ake rike dasu da Mayakan sa kai na kasar 285 da ‘yan tawayen ke rike dasu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.