Isa ga babban shafi
Yemen

Yarjejeniyar tsagaita wuta na aiki a Yemen

Bisa dukkan alamu a yau Litinin, yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Yemen duk da an samu rikici a wasu yankunan kasar. Ana ganin lafawar rikicin karkashin yarjejeniyar haske ne ga tattaunawar sulhu da ake shirin gudanarwa a makon gobe da nufin kawo karshen rikicin kasar.

Dakarun Yemen da ke goyon bayan gwamnatin kasar
Dakarun Yemen da ke goyon bayan gwamnatin kasar REUTERS/Fawaz Salman
Talla

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta soma aiki ne tun a tsakiyar dare a Lahadi.

Bangaren gwamnatin shugaba Abedrabbo Mansour Hadi da bangaren ‘Yan tawayen Huthi yan shi’a da suka kore shi daga fadar shi a Sanaa dukkaninsu sun yi alkawalin mutunta yarjejeniyar da kuma Saudiya da kawayenta da ke luguden wuta akan ‘yan tawaye sun amince su dakatar da kai hare hare karkashin yarjeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta.

Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya ce mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar kamar wani tsani ne da zai kai ga tabbatar da zaman lafiya a Yemen.

Sai dai bangaren gwamnati sun zargi ‘yan tawaye da kai hare hare a biranen Taez da Marib da Sanaa.

An dade bangarorin da ke rikici a Yemen na rusa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Rikicin Yemen dai ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tursasawa miliyoyan mutanen kasar gujewa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.