Isa ga babban shafi
Amurka

Trump yayi amai ya lashe

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin Jam’iyyar Republican Donald Trump yayi amai ya lashe, inda yace batun zargin da ya yiwa Shugaba Barack Obama da Hillary Clinton na kafa kungiyar IS da wasa yake.

Trump ya zargi 'yan jarida da yi masa kage
Trump ya zargi 'yan jarida da yi masa kage (Reuters)
Talla

Kamar dai yadda ya saba, Donald Trump ya zargi kafafen yada labarai da yiwa kalamansa gurguwar fahimta, inda yace sun rawaito ba dai-dai ba.

A lokacin gangamin yakin neman zaben sa a Florida ne Trump ya Ambato sunayen Obama da Hillary dake takara a Democrat a matsayin masu taimakawa IS, tare da sake maimata hakan a wata hirar da yayi jiya alhamis.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.