Isa ga babban shafi
Amurka

Trump bai cancanci jagorantar Amurka ba-Obama

Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya bayyana dan takarar neman shugabancin kasar karkashin jam`iyyar adawa ta Republican Donald Trump a matsayi wanda bai cancanci shugabancin kasar ba.

Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya soki Trump
Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya soki Trump REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Obama ya ce yana mamakin yadda har yanzu j`iyyar Republican ke marawa Trump din baya a takarar tasa ta neman shugabancin kasar.

Shugaban kasar Amurkan ya ce duk da a baya ya samu banbancin manufofi tsakaninsa da yan takarar Jam`iyyar Republican, bai taba daukarsu a matsayin wadanda zasu gaza wajen jagoranci ba.

Donald Trump na shan suka bisa batanci ga wasu daga cikin iyayen sojin Amurka da suka mutu a fagen fama, sai kuma goyon bayansa da ya nuna ga kasar Rasha bisa manufarta kan yankin Crimea.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.