Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka na zargin Rasha da nuna goyon baya ga Trump

Gwamnatin Kremlin ta musanta zargin katsalandan ga harakokin siyasar Amurka, bayan Shugaba Barack Obama ya ki yin watsi da zargin cewa Rasha na kokarin ganin Dan takarar Republican Donald Trump ya kai ga nasara.

Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka
Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka REUTERS
Talla

Amurka na zargin Rasha ne da kokarin yin zagon kasa ga yakin neman zaben ‘yar takarar democrat Hillary Clinton na fallasa wasu bayananta na email da Wakileaks ya bankwado.

Wannan kuma ya dada fito da tsamin dangantaka da ke tsakkanin Rasha da Amurka musamman zamanin mulkin Obama na Democrat da kuma Vladimir Putin.

Shugaba Putin na Rasha dai ya musanta zargin, inda ya ce ba su taba sa bakinsu akan abin da ya shafi harakokin siyasar cikin gidan wata kasa ba.

Sai dai kuma shugaba Obama na Amurka ya ce komi na iya faruwa, domin ba karamin aikin Rasha ba ne musamman ta la’akari da yadda dan takarar Republican Donald Trump ke yabon tsarin shugabancin kasar.

Obama ya ce suna sane akan Rasha ta tatsi bayanansu, amma ya ki bayyana dalilan da ya ke ganin ya sa Rasha ta yi tonon sililin da wikileaks ya bankado akan sakwannin email din Hillary Clinton.

Trump dai ya dade yana sha’awar tsarin mulkin Putin al’amarin da wasu masharhanta ke ganin shi ya sanya Rasha ke mara ma shi baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.