Isa ga babban shafi
Amurka

Dole ne Clinton ta zama shugabar kasa- Sanders

Sanata Bernie Sanders da ya sha kaye a zaben fidda gwani, ya bukaci mambobin jami’iyyar Democrat da su mara wa Hillary Clinton baya don ganin ta samu shiga fadar White House a matsayin shugabar kasar Amurka.

Sanata  Bernie Sanders ya goyi bayan Hilary Clinton don ganin ta samu shugabancin Amurka a zaben kasar mai zuwa
Sanata Bernie Sanders ya goyi bayan Hilary Clinton don ganin ta samu shugabancin Amurka a zaben kasar mai zuwa REUTERS/Gary Cameron
Talla

Sanders wanda ya sha kaye a hannun Clinton, ya bukaci haka ne a jawabin da ya gabatar a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa a Philadelphia.

Mahalarta taron sun bige da murna bayan Sanders ya ce, dole ne Hillary Clinton ta zama shugabar kasar Amurka.

Gabanin jawabin nasa, magoya bayan Sanders sun nuna adawarsu karara ga Mrs. Clinton wadda za a tabbatar da ita a matsayin ‘yar takarar Democrat a ranar Alhamis mai zuwa a babban taron.

Ita ma uwargidan shugaban Amurka, Michelle Obama ta gabatar da jawabi mai tayar da tsimi, inda ta yi hannunka mai sanda wajen caccakar dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.