Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ta dauki Kaine Mataimaki

‘Yar takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar Democrat a Amurka Hillary Clinton ta dauki Tim Kaine Senata daga Jihar Virginia a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Hillary Clinton da Tim Kaine 'Yan takarar shugabancin Amurka a Jam'iyyar Democrat
Hillary Clinton da Tim Kaine 'Yan takarar shugabancin Amurka a Jam'iyyar Democrat SAUL LOEB / AFP
Talla

Zaben mataimakin dai na zuwa duka saura kwanaki uku jam’iyyar Democrat ta gudanar da babban taronta a Philadelphia inda za a tabbatar da Hillary Clinton da kuma Tim Kaine a matsayin ‘Yan takarar jam’iyyar.

Clinton ta sanar da daukar tsohon gwamnan na Virginia ne a Twitter da kuma sakon kwarta ka kwana zuwa ga magoya bayanta.

Tuni abokin hamayyarta Donald Trump ya dauki Gwamnan Jihar Indiana Mike Pence a matsayin dan takarar mataimakinsa.

Firaministan kasar Hungary Viktor Orban ya kasance shugaba na farko daga Tarayyar Turai da ya marawa dan takarar Republican Donald Trump baya.

A cikin wani jawabi da ya gabatar a Romania a yau Asabar, Mr Orban ya ce Donald Trump ya fi Hillary Clinton cancanta, musamman ga manufofin Turai da kuma hungary.

Firaministan na Hungary na da ra’ayi guda da Trump akan kyamar kwararar bakin haure da ‘Yan gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.