Sanders ya goyi bayan Clinton ta Amurka
Sanata Bernie Sanders da ya fafata da Hillary Clinton wajen neman takarar shugabancin Amurka a karkahsin Jam’iyyar Democrat ya bayyana goyan bayansa ga Clinton a wajen wani taron gangami da aka gudanar yau a New Hampshire.
Wallafawa ranar:
Sanders wanda ya yaba wa shugaba Barack Obama kan rawar da ya taka wajen fitar da kasar daga halin matsalar tattalin arzikin da 'yan Republican suka jefa ta, ya ce a shirye yake ya yi aiki da Clinton wajen ganin sun samu nasara a zabe mai zuwa don samar da ci gaba.
Sanata Sanders ya ce ya zama dole Clinton ta zama shugabar Amurka domin aiwatar da shirye-shirye masu inganci da za su daga darajar Amurka da kuma inganta rayuwar Amurkawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu