Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ta caccaki Trump kan kyamar Yahudawa

Hillary Clinton da ke takarar shugabancin kasa a jam’iyyar Democrat a Amurka ta caccaki abokin hamayyarta na Republican Donald Trump kan wasu kalamansa na kyamar yahudawa da ya wallafa a shafin Twitter.

Hillary Clinton ta Democrat
Hillary Clinton ta Democrat REUTERS/Aaron Josefczyk
Talla

Donald Trump na Republican ya fara wallafa hoton Hillary Clinton ne a Twitter, hoton da ya munanata a matsayin mai laifin rashawa.

Daga baya kuma ya sake wallafa kalaman da ke cewa hoton ya yi kama da tambarin yahudawa da ake kira star of David.

Daga bisani Trump ya goge hoton a twitter tare da musanya wa da wani.

A martanin da ta mayar abokiyar hamayyar shi Hillary Clinton ta Demorat ta caccaki attajirin wanda ta ce ya dauko hoton ne daga wani shafin intanet na masu kyamar yahudawa.

Clinton tace hakan ya nuna yakin neman zaben shi ya fara wuce gona da iri, kamar yadda ofishin yakin neman zabenta ya ce dama ce ga masu jefa kuri’a su san wanda zasu zaba shugabansu.

Yanzu haka dai ana ta yada kalaman na Trump a Twitter duk da ya goge a shafin shi.

Ana sa ran shugaban kasar Amurka Barack Obama zai shiga tawagar yakin neman zaben Hillary Clinton a yau Talata domin samar wa ‘Yar takarar ta Democrat karin magoya baya a shirin fafatawar da ta ke yi Donald Trump Republican.

Obama da Clinton zasu halarci Charlotte a jirgin shugaban kasar da ake kira Air Force One.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.